1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kenya: Arangama tsakanin 'yan sanda da matasa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 25, 2024

Masu zanga-zangar karya shingen jami'an tsaron tare da kutsawa cikin zauren majalisar dokokin kasar

https://p.dw.com/p/4hTq0
Hoto: Monicah Mwangi/REUTERS

Arangama ta barke a Nairobi babban birnin kasar Kenya a Talatar nan, tsakanin 'yan sanda da matasa masu zanga-zangar nuna adawa da sabuwar dokar karin haraji da shugaba William Ruto ya gabatar, inda 'yan sandan suka rinka harba hayaki mai sa hawaye da kuma harsasan roba ga matasan.

Karin bayani:Shugaba Ruto na Kenya ya nemi ganawa da masu zanga-zanga

'Yan sandan dai sun datse hanyar shiga majalisar dokokin kasar, wadda ke tafka muhawara kan kudurin karin harajin domin amincewa da shi.

Kuma tun a makon da ya gabata ne daruruwan matasan suka fantsama kan titunan Nairobi don nuna tirjiya da bijirewa wannan sabon tsari, da suka ce zai kara jefa al'ummar kasar cikin gararin rayuwa.

Karin bayani:Matasa sun kira yajin aikin gama gari a kasar Kenya

Yanzu haka dai masu zanga-zangar sun karya shingen jami'an tsaron, inda suka kutsa cikin zauren majalisar dokokin kasar, bayan da 'yan majalisar suka amince da dokar karin harajin.