Rikici a jam'iyyar APC na illa ga makomarta a 2019
February 27, 2018Duk da cewar sun nasarar kara tsawon wa'adin mulki na shugabancin jam'iyyar har ya zuwa bayan zaben tarraya na badi, daga dukkan alamu har yanzu da sauran rina cikin kabar 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki da suka kamalla wani babban taro na majalisar zartarwa ta kasa a cikin kallon kallo.
Babbar matsalar jam'iyyar dai na zaman iya kaiwa ga sulhunta tsakanin 'ya'yanta da suka yi nasarar karbar mulki amma kuma ke neman karewa dutse a cikin riguna tsakanin juna.
Burin karbar mulki da ma barazana ga kujera dai na zaman ummul'aba'isin babban rikicin da ya kai ga kafa kwamitin tsohon gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu.
To sai dai kuma an kamalla babban taron na kasa ba tare da alamun nasara a bangarorin rikicin da kusan kowa ke kan dokin naki kuma ke fadin ko hanyarsa ko kafar katako. Can a Kaduna dai gwamnan jihar Nasir El-Rufa'i ya ce bashi shirin tattaunawa da masu sana'a ta ta'addanci a cikin APC. A yayin kuma da a Kano masu goya bayan gwamnan ke fadin ko limancin Ganduje ko a sauya masallaci a fadar Hon. Alhassan Ado Doguwa da ke zaman mai tsawatarwa a majalisar wakilan Tarrayar Najeriya.
Ko ya take shirin kayawa a tsakanin masu shirin bin limamai da masu kokarin sauya masallatan dai, can a jihar Bauchi dai akwai alamun sassautowa a tsakanin 'yan majalisar wakilai na jihar da kuma gwamnan Mohammed Abdullahi Abubakar da ke fadin damina ta fara nuna alamun sauka a siyasa ta jihar.
To sai dai kuma a fadar Sanata Abdullahi Adamu da dattawan suka tsige a bisa goyon baya ga shugaban kasar makonni biyu baya ya ce har yanzu a kwai sauran fata a kokari na dinke barakar.