1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rayuwa ta tsananta a Yemen

October 29, 2017

Majalisar Dinkin Duniya ta damu kan karuwar bukatar jin kai a kasar Yemen tana mai kiran da a rungumi dokokin tausayawa juna na kasashen duniya, tsakanin bangarorin da ke fada da juna.

https://p.dw.com/p/2mh1q
Jemen Kind Unterernährung
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Mohammed

Shugaban ayyukan agaji na MDD Mark Lowcock ya bayyana damuwa kan karuwar bukatar jin kai a kasar Yemen mai fama da rikice-rikice, yana mai kiran da a rungumi dokokin tausayawa juna na kasashen duniya, tsakanin bangarorin da ke fada da juna. Yayin da yake kammala wata ziyarar kwanaki biyar da ya kai kasar ta Yemen, Mr. Lowcock ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen yaki a kasar, tare da girka tsarin jagoranci irin na siyasa.

Kasar ta Yemen dai na fama da matsananciyar annobar cutar kwalara da ba a taba ganin muninta ba a duniya ga kuma uwa-uba karancin abinci. Ana sa ran babban jami'in na MDD zai gabatar da wani jawabi a wani babban taro da zai dubi matsalolin da ke a Yemen din, wanda za a yi a yau Lahadi a birnin Riyahd na kasar Saudiyya.