1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da Turkiyya sun kulla wata alaka

April 8, 2019

Kasashen Rasha da Turkiyya sun kulla awata alaka ta fuskar yaki daidai lokacin da Amirka ke adawa da shirin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/3GTfR
Russland Moskau Treffen Wladimir Putin und Tayyip Erdogan
Hoto: Reuters/Kremlin/A. Nikolsky

Shugaba Putin na kasar Rasha ya zanta da takwaransa na Turkiyyar Racep Tayip Erdogan dangane da cinikin manyan makaman nan masu linzami samfurin S-400 da suka sanya wa hannu.

A ganawar da suka yi a ranar Litinin, shugabannin sun kuma kulla kawance ta fuskar dabarun yaki, al'amarin kuma da ke tayar wa kasar Amirka hankali.

Shugaba Putin ya ce batun kai wa Turkiyya manyan makaman cikin watan Yulin bana, shi ne babban abin da ya bai wa fifiko a yanzu.

Karo na uku ke nan a bana Shugaba Erdogan na Turkiyya ke kai wa Mr. Putin na Rasha ziyara.