Putin da Erdogan sun gana a St. Petersburg na Rasha
August 9, 2016Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya na yin ziyara a Rasha inda ya gana da takwaran aikinsa shgaba Vladmir Putin na Rasha.
Hulda ta sake daidaituwa tsakanin Rasha da Turkiyya
Wannan ziyara ta shugaba Recep Tayyip Erdogan a birnin St. Petersburg na kasar Rasha na zaman wani mataki na sake sassantawa tsakanin kasashen biyu wadanda suka kwashe watannin tara suna yin zaman doya da man ja, bayan da Turkiyya ta kakapo wani jirgin saman yaki na Rasha a cikin watan Nuwamba da ya gabata a kan iyakarta da Siriya tare da kashe matukin jirgin.A cikin watan Yuni da ya gabata ne Rasha ta ce ta samu sakon shugaban Turkiyya wanda a cikin ya nemi afuwa a game da lamarin da ya faru tare da bayyana takaicinsa da kuma fatan neman ganin an sake daidaita hulda tsakanin kasashen biyu.Kuma tun da farko shugaba Vladmir Putin ya dage takunkumin karya tattalin arziki da Rasha ta kakkaba wa Turkiyya a kan sha'anin yawon bude ido da kuma huldar kasuwancin.
Shugabannin biyu za su tattauna batun yakin Siriya
A Lamari na baya-baya nan da ya afku a Turkiyya na yunkurin juyin mulki da ya ci tura.Shugaba Vladmir Putin shi ne na farko daga cikin shugabannin kasashen duniya da ya kira Recep Tayyip Erdogan ta wayar tarho cewar yana fatan ganin al'amuran sun sake daidaita da gaggawa a Turkiyyan.Kuma wannan ziyara ta shugaban na Turkiyya a Rasha na zaman wata barazana ga kasashen yammacin duniya a cewar Alexander Baunov babban editan wata jaridar ta gwamnatin Rasha.Ya ce: ''Duk wata kasa da ta kusanci Rasha dole ne wasu kasashe su firgita kuma wannan ganawa da aka yi tsakanin Putin da Edogan wani babban misali ne na daidaituwar hulda tsaknin Rasha da Turkiyya.Shugaba Vladmir Putin dai ya ce ganawar da suka yi da shugaban Turkiyya wanda ya amince ya karbi bakwancinsa wata babbar niyya ce ta ganin kasashen biyu sun sake kula hulda bayan irin abin da ya faru a baya. Ko da shi ke ma dukkanin shugabannin biyu suna da sabanin ra'ayoyi a kan yakin Siriya amma Alexander Baunov ya ce za su iya samu fahimta juna a kan matsaya daya a game da yakin Siriya.Ya ce: ''A yanzu babu wani abin da suka fada a kan yakin Siriya amma su dukkaninsu sun amince cewar za su yi wani abu ba tare da ganin an samu wata baraka ba a tsakaninsu a game da batun na Siriya.''
Recep Tayyip Erdogan dai ya sha cewar ya zama tilas shugaba Bashar al Assad na Siriya ya yi marabus yayin da shugaban Rasha ke da sabanin ra'ayin haka. Kwararru na kallon cewar wannan sabuwar hulda tsakanin Turkiyya da Rasha za ta bai wa Rashan kwarin gwiwa musammun ma a daidai lokacin da dangantaka tsakanin Rasha da Amirka da kuma Kungiyar Tarayar Turai ta dagule sakamakon yadda Rasha ke da hannu a yakin da ake yi a Ukraine da kuma Siriya.