1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta kaddamar rigakafin zazzabin cizon sauro

September 21, 2024

A hukumance Jamhuriyar Nijar ta kaddamar aikin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro da ya jima yana hallaka rayuka a Afirka. Nijar din dai ta kasance kasar farko da ta yi haka a yammacin Afirka da ta fara.

https://p.dw.com/p/4kviC
Alluran rigakafin cutar Maleriya
Alluran rigakafin MaleriyaHoto: Brian Ongoro/AFP

Jamhuriyar Nijar ta zama kasar farko a yankin yammacin Afirka, da ta fara amfani da alluran rigakafin cutar zazzabin cizon sauro wato maleriya a hukumance, domin ganin ta yi yaki cutar da ta jima tana kashe yara kananan gami da manya a kasashe matalauta.

A ranar Alhamis da ta gabata ne dai aka kaddamar da rigakafin mai girma a yankin Gaya da ke kudu maso yammacin Nijar din, yankin kuma da cutar ta jima tana ta'adi, kamar yadda ministan lafiya na kasar Garba Hakimi ya tabbatar.

Sama da mutum dubu 600 ne dai cutar Maleriya ta kashe a shearar 2022 kadai a duniya, kuma 95% na wannan adadin sun mutu ne a Afirka.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta ce 80% na wadanda suka mutun kuwa, kananan yara ne daga haihuwa zuwa shekara biyar.

A shekara ta 2022 ne aka amince da rigakafin cutar Maleriya da kamfanin GSK na kasar Burtaniya ya samar.