Nijar ta janye daga harkokin kungiyar Francaphonie
December 26, 2023Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyar Nijar ta dakatar da kasar daga alaka da duk wasu harkoki masu alaka da kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransanci ta Francaphonie.
Gwamnatin ta Nijar ta ce dama makasudin kafa kungiyar bai wuce saboda neman kare muradun kasar Faransa ba ne.
Matakin na kuma zuwa ne yayin dangantaka ke kara tsami tsakanin Nijar din da Faransa da ta yi mata mulkin mallaka a baya.
Kungiyar ta Francaphonie dai ta nuna cewa burnita shi ne bunkasa harshen Faransanci a tsakanin kasashe na duniya, sai dai kuma galibin kasashen da ke cikin kungiyar, kasashe ne da Faransar ta yi wa mulkin mallaka.
Cikin watan Yulin da ya gabata ne dai sojoji suka kifar da gwamnatin dimukuradiyya a Nijar, abin da ya janyo rashin jituwa tsakaninta da kasashen yammacin duniya ciki har da Faransa.