Kudin takara a jam'iyyar APC a Najeriya
September 3, 2018Fitar da adadin kudin da 'yan takarar za su biya da jam'iyyar APC da ke mulki ta yi, wanda ya nuna cewa mai neman takarar majalisar jiha zai biya Naira milyan daya, 'yan majalisar tarayya kuma milyan uku da dubu 300, sai sanata miliyan takwas da dubu 500 gwamna kuwa zai biya miliyan 22 da dubu 500 dan takarar shugaban kasa kuwa ya biya miliyan 55 da dubu 500, ya nuna ya fi kudin takaradar takarar dukkanin sauran jamiyyun. Tuni 'yan takara suka kai ga bara da ma neman lallai a sake lale. Malam Adamu Garba matashi ne da ke neman takarar shugaban kasa a jamiyyar APC mai mulkin, ya ce sun aika sako ga jam'iyyar.
Ga matasan Najeriyar da suka yi gwagwarmayar samun doka da ta rage yawan shekarun tsayawa takara ga matasa wato "Not Too Young to Run", sun nuna damuwa a kan kudaden da aka sanya ga 'yan takara da suke ganin zai kawo masu cikas. To ko wacce illa wannan zai iya yi ga tsarin siyasar Najeriyar da dama aka dade ana nuna damuwa na yawan amfani da kudi? Mallam Abdulrahman Abu Hamisu masanin siyasa ne a cibiyar nazarin dimukuradiyya da ke Abuja, a cewarsa hakan ya rusa sabon tsarin nan na "Not Too Young to Run", da aka yi saboda matasan da ke son tsayawa takara wanda da yawansu ba su da wannan kudin, kuma zai ma iya kara matsalar cin hanci da rashawa domin duk wanda ke so sai ya yi kokarin ganin ya tara.
Jam'iyyar APC dai ta yi gum a kan batun kan cewa tana can tana taro na kwamitin zartaswarta. Batun yawan kudin da ake kashewa a fannin tsayawa takara a Najeriya, na zama babban al'amari da ke kawo cikas musamman ga mutanen da ba su da galihu, amma kuma suke ganin suna da gudummawar da za su bayar a harkar siyasar Najeriyar.