1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matan Najeriya na shirin samun nasara

Uwais Abubakar Idris LMJ
March 9, 2022

A wani matakin da ke nuna samun nasara ga matan Najeriya da suka kwashe kwanaki suna zanga-zanga, majalisar wakilan kasar ta yi kwana a kan kudurori guda uku da suka shafi matan da a baya ta yi watsi da su.

https://p.dw.com/p/48Egi
Ranar Mata ta Duniya I 2022 I Najeriya
Matan Najeriyar sun kwashe kwanaki suna zanga-zanga da matakin majalisar na bayaHoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

A yanzu dai majalisar wakilan ta bayyana amincewa da wadannan kudirori, domin karawa matan karfi wajen damawa da su a harkokin siyasar kasar. Majalisar wakilan Najeriyar dai ta yi aman ta lashe ne, bayan da ta fuskanci fito na fito tsakaninta da matan Najeriyar musamman ma kungiyoyin da suke gaba wajen kare hakokinsu kasar. 'Yan majalisar wakilan sun amince da sake duba kudurorin uku da suka yi watsi da su, wadanda suka hadar da batun bai wa matan kaso 35 cikin 100 na madafan iko a harkokin siyasa.

Karin Bayani: Matan Najeriya na yunkurin kwato hakkinsu

Shugaban majalisar wakilan Najeriyar Femi Gbajabiamila ne dai ya jagoranci amincewa da wannan matakin, kuma tuni matan Najeriyar da suka fita a jihohi da dama suna zanga-zangar lumana a kan lallai sai majalisar ta sake duba lamarin suka fara tsallen murna. Sannu a hankali ana kara ganin karuwar jajircewa da matsin lamba da a Tarayyar Najeriyar, domin anga irin wannan a lokacin da matasa suka yi tasu fafutukar har sai da aka samar da doka.

Da wannan mataki da majalisar wakilan Najeriyar ta dauka ya nuna a yanzu sun sha bam-bam ko an samu sabanin tsakaninta da ta dattawa, to sai dai shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ya ce akwai bukatar fahimtar abu guda: "Batun daidaitawa ba zai iya zama abin yi ba, in aka zo maganar gyaran fuska ga kundin tsarin mulki. Sashi na biyar na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa majalisar wakilai ikon ta yi aiki bisa tsarinta, kuma mun dogara a kan wannan sashi mun daidaita bambancin da ke tsakaninmu da majalisar dattawa."

Karin Bayani: Rudani a fagen siyasar Najeriya

To sai dai  in an zo duba wadannan sassa ne za a san kaso nawa ne majalisar za ta bai wa matan Najeriya da suka dage sai an basu kaso 35 cikin 100 na mukaman siyasa, a yayin da ake jiran matakin da majalisar dattawa za ta dauka da matan suka ce za su ci gaba da matsawa domin tabbatar da hakarsu ta cimma ruwa.