Mai digiri ne zai yi mulki a Najeriya
February 9, 2022Kama daga fari zuwa baki zuwa ga rodi-rodi dai, Tarayyar Najeriyar ta shafe shekara da shekaru tana samar da shugabanni iri-iri a matakai dabam-dabam. To sai dai kuma kafin sheakara ta 2007, daukacin shugabannin kasar na karewa ne da ilimin da bai wuce na kamalla makamarantar sakandare ba. Sai dai kuma wata sabuwar doka da majalisar wakilan kasar ta ce tana shirin ta kafa domin ingantar mulki, ta tanadi matakin digiri a matsayin mafi karancin ilimin kai wa ga zama shugaban kasa ko gwamna. Ya zuwa yanzun dai kundin tsarin mulkin Najeriyar ya tanadi matakin gama makarantar firamare ne, a matsayin sharadin tsayawa kowace irin takara a kasar.
Ana dai zargin rashin wadataccen ilimin, a matsayin babban dalilin da ke janyo kasawar shugabannin kasar iya goga kafada a ko'ina a duniya, kuma ko cikin tsarin shugabancin kasar batun ilimin na da ruwa da tsaki da tasirin da ake kallo a mulkin tsohuwar gwamnatin Umaru Yar'Adua da ke zaman ta farko wadda mai matakin digirin ya zama shugaban kasa. Ko ma wanne tasiri neman fifita batun boko a cikin tsarin siyasa da tsayawa takara a Najeriyar ke shirin haifarwa, kuskure ne babba dora batun boko a cikin neman mulkin a tunanin Barrister Buhari Yusuf lauya mai zaman kansa a Abuja fadar gwamnatin kasar. Abun jira a gani dai na zaman yadda take shirin kayawa a tsakanin masu kallon 'yancin da masu fatan boko a cikin rikicin neman mulkin Najeriyar.