1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kamarin cin hanci da rashawa

January 9, 2024

Dakatar da wasu jami'an gwamnati biyu da kuma korar ministar jin kai ya kara fito da girman matsalar cin hanci da rashawa da ta yi katutu a cikin gwamnati

https://p.dw.com/p/4b1l9
Shugaban Najeriya Bola Tinubu yayin gabatar da kasafin kudi a Majalisa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu yayin gabatar da kasafin kudi a MajalisaHoto: Ubale Musa/DW

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu wanda ya dakatar da ministar jin kai Betta Edu daga mukaminta don gudanar da bincike ya na da jan aiki kan yanke hukunci bisa yadda aka samu karin jami'ai tare da kamfanin wani minista a gwamnatin da amfana daga kwangila a ma'aikatar jin kan da ke zaman cibiyar badakalar cin hanci ta kasar.

Sama da Naira miliyan 438 ne dai wani kamfani da mai dakin Tunji Ojo ministan cikin gidan tarraya Najeriyar ke da wakilci a ciki, ya yi nasarar samu daga wata kwangila ta shawara ga batun jin kan da ke neman rikidewa zuwa jin kai cikin kasar.

Karin Bayani: Yunkurin dakile cin hanci a Najeriya na gamuwa da cikas

Shugaban da ke kokawar wanke sunansa bisa zargin hancin a daukacin rayuwar siyasar dai daga dukkan alamu yana tsakanin mayar da hankali kan babban yakin cin hancin da ya maimaye daukacin harkokin kasar.

Farfesa kamilu Sani Fagge kwarrare kan harkar mulki a kasar, ya ce da kamar wuya, iya yin tasiri a banagren Tinubun ga batun cin hancin da ke da alamun komawa ruwan dare gama duniya.

Kama daga batun siyasa ya zuwa rayuwa da kila ma makomar kasar,  tarrayar Najeriyar ta dauki lokaci tana ji a jiki a cikin annobar cin hanci da asarar da ta kai dalar Amurka miliyan dubu 600 tun daga yancin kasar.

Karin Bayani: Najeriya: Gwamnati na yakar cin-hanci

Sai dai kuma matakin Tinubun ya fara daukar hankalin yan kasar da daman gaske da ba kasafai suke ganin hukunci bisa yan bokon da ke a kan gaba cikin sana'ar hancin ba.

A fadar Mahdi Shehu da ke sharhi kan batun yan mulkin, babu shiri na zahiri a bangaren gwamnatin da sunan yaki da cin hanci kama daga alkalai zuwa 'yan doka dai a shekarar bana ana kallon ninka kudin kasafi na masu ikon tarrayar Najeriyar a wani abun da ke zaman alamun danyen ganye na mulkin kasar.