1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsarin hana fitar da tsabar kudi daga banki

Uwais Abubakar Idris
April 5, 2023

Gwamnonin Najeriya sun yi wani taro da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa da kuma wakilan babban bankin kasar a kan tsarin hana fitar da tsabar kudi daga asusun gwamnati.

https://p.dw.com/p/4PjJN
NO FLASH Zentralbank von Nigeria
Hoto: public domain

Taron dai tsakanin wadanan shugabanin hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na Najeriyar gwamnonin jihohin kasar 36 ne ya biyo bayan nuna rashin amincewa da wannan tsari da gwamnonin suka yi ne tun lokacin da hukumar yaki da laifuffukan kudadde ta Najeriyar ta fitar da wannan umurni.

Bayanai sun tabbatar man cewa an gudanar da taron kuma an tattauna batutuwa da suka shafi batun kudin tsaro da gwamnoni da sabon tsarin da ya hana fitar da tsabar kudi a asusun gwamnati sai dai a aika ta banki, batun da ya haifar da tirjiya.

To sai dai bayan kamala taron gwamnonin sun ki cewa uffan a kan abinda suka tattauna haka nan jami'an da ke magana da yawunusu, amma akwai ta bacin cewa sun samu shawo kan hukumomin sun daga masu kafa na lokacin da ya kamata a fara aiwatar da wannan sabon tsari daga 1ga watan nan zuwa 29 ga watan mayu lokacin da sabbin gwmnoni 19 da aka zaba zasu kama aiki yayinda 17 zasu fara wa'adinsu na biyu.

Batun kudadden da gwamnonin kan kebe domin ayyukan tsaro sun dade suna haifar da kace-nace tare da nuna 'yar yatsa a kan wannan batu da ma zargin cin hanci da rashawa. Tun a watan Janairun wannan shekara ne dai hukumar yaki laifuffukan da suka shafi kudadde ta Najeriyar ne ta yi garghadin cewa duk jami'in gwamnati da ya karya sabuwar kaidar zai fuskanci hukunci.

Da alamun dai akwai sauran aiki a gaba domin duk da kariyar da gwamnonin Najeriyar ke da shi tuni wasun su ke takun saka da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa saboda zargi na cin hanci da ya sa gwamnonin ke son amfani da kungiyarsu don samun mafaka da ma taya su fada amma kuma kungiyar ke nokewa a yanayi na kowa tashi ta fisshe shi.