Fargabar karuwar ambaliya a Najeriya
August 10, 2021Kama daga tituna da gadoji da ma uwa uba gidajen al'umma dai, sannu a hankali ambaliyar ruwa na bazuwa a sassan Tarayyar Najeriyar dabam-dabam. Kuma ya zuwa kawo yanzu, kimanin jihohi 28 da kananan hukumomi 121 ne ambaliyar da ke yin barazana ta shafa a kasar. To sai dai kuma Abujar na kara kwantar da hankula tare da ayyana lafiyar madatsain ruwan da a baya ke zaman na kan gaba a fashewa da tafka barna a gonaki da gidajen al'umma.
Karin Bayani: Ambaliyar ruwa na ci gaba da barna a Najeriya
Ministan ruwan kasar Injiniya Sulaiman Adamu ya ce, mafi yawan madatsun ruwa 323 da kasar ke takama da su na da ingancin da ba su zama barazana ga makomar al'umma ba. Kama daga Jebba ya zuwa madatsar Lagdo dai, a baya Najeriyar ta kirga asara mara adadi sakamakon fashewar madatsun ruwan da kan wanke gonaki a sassa dabam-dabam na arewacin kasar. Ko a bara kadai dai, Najeriyar ta fuskanci karancin shinkafa sakamakon Ambaliyar da ta shafi jihohin Kebbi da 'yar uwarta Jigawa.
To sai dai kuma a fadar Dakta Mahmud Mohammed da ke zaman ministan muhallin Najeriyar, matsalar ta ambaliya cikin kasar na da ruwa da tsaki da tsohuwar al'ada a kasar. Gayawa kunne a cikin neman tserar da jiki, ko kuma gani ga wane da ya ishi wane dai, tuni manyan biranen kasar suka fara nazari kan ambaliyar da ta janyo asara mai girma a jihohin Taraba da Legas da kuma jihar Nasarawa.
Karin Bayani: Ambaliya na janyo asarar rayuka a Najeriya
Kuma a tunanin Dakta Aliyu Barau da ke zamman masani na muhalli a jam'iar Bayero a Kano, akwai jan aiki a bangaren hukuma da su kansu 'yan kasa da nufin kauce wa barazanar da tai ta'adi har a manyan kasashen duniya. Sama da mutane 430 ne dai suka rasa rayukansu, ko bayan raba sama da mutane dubu 500 da muhalli a shekara ta 2012 sakamkon ambaliyar ruwan a Najeriya.