1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ambaliya ta jaza rasa rayuka a Najeriya

July 17, 2018

Mahukunta a jihar Katsina sun samu rahotanni cewa ruwan da ya haddasa ambaliya ya tafi da wasu gawarwaki zuwa Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/31aN4
Katsina Flut Nigeria
Hoto: DW/Y. Ibrahim

Mutane 38 sun halaka sama da gidaje 500 sun lalace sakamakon ambaliyar ruwa a karamar hukumar Jibiya da ke jihar Katsina, mahukunta a jihar ta Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya sun samu rahotanni cewa ruwan ya tafi da wasu gawarwaki zuwa Jamhuriyar Nijar. Yanzu haka dai mutane da dama na neman mafaka gun 'yan uwa da abokan arziki.

Flut Nigeria Afrika 2010 Flash-Galerie
Zama cikin zulumiHoto: AP

Wannan iftila'i dai ya faru ne sakamakon ruwan sama da aka kwana ana yi a garin na Jibiya da ke jihar Katsina. Dr. Aminu Garba waziri shi ne shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Katsina ya tabbatar da afkuwar lamarin da kuma kididdigar adadin rayukan da aka rasa. Sai dai wasu na ganin akwai sakaci na samar da isassun magudanan ruwa dan ba wa ruwa hanyarsa.

Jihar Katsina dai na daga cikin Jihohin da ke yawan fama da iftila'in ruwan sama a Najeriya.