1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sun mutu a hadarin jirgin ruwa a Siriya

September 23, 2022

Wani hadarin jirgin ruwa da ke dauke da bakin haure 'yan kasashen Labanan da Siriya, ya yi sanadin salwantar gomman rayuka a Tekun Bahar Rum. Sama da mutum 100 ne ke ciki.

https://p.dw.com/p/4HGBW
Syrien | Rettungsaktion am Hafen von Tartous
Hoto: Saleh Sliman via REUTERS

Akalla bakin haure 73 ne rahotanni ke tabbatar da mutuwarsu bayan wani jirgin ruwan da ke dauke da su daga Labanan ya nitse a Tekun Bahar Rum, a cewar ma'aikatar lafiya ta kasar Siriyar.

Hukumomi sun ce kimanin mutum 150 galibin su 'yan kasashen Labanan da kuma Siriya ki cikin jirgin da nitse a ranar Alhamis a tekun.

Wannan ne dai hadarin ruwa mafi muni da Labanan musamman ta gani, tun wani makamancinsa da ya auku shekaru uku da suka gabata.

Jami'an lafiya a yankin Tartus inda hadarin ya faru, sun ce sun sallami wasu da suka tsira a ibtila'in.

Galibin wadanda lamarin ya rutsa da su dai sun fito ne daga yankunan marasa galihu a Labanan din da kuma Siriya.