1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MDD ta zargi Morocco da Spaniya ta cin zafari

June 28, 2022

Bayan mutuwar wasu bakin haure da ke kokarin kutsawa Turai ta iyakar Moroko da Spaniya, Majalisar Dinkin Duniya ta soki ayyukan hukumomi a iyakan kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/4DNk6
Spanien Melilla | Migranten in der spanischen Nordafrika-Exklave Melilla
Hoto: Javier Bernardo/AP/picture alliance

Majalisar Dinkin Duniya, ta yi Allah wadai da abin da ta kira amfani da karfi fiye da kima da hukumomi ke yi a iyakar Spaniya da Moroko, tare da nuna bukatar cikakken bincike a kan kisan wasu bakin haure su 23 a makon jiya.

Kimanin wasu bakar fata mutum dubu biyu ne suka yi kokarin ketare iyakar Morokon da nufin shiga Spaniya, abin da ya haddasa husuma a ranar Juma'ar da ta gabata.

Satatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ta bakin kakakinsa Stephane Dujarric, ya ce mutanen da ake ci musu zarafin a wajen, na da hakkin da dole ne a kiyaye musu.

Mr. Guterres ya kuma tabbatar da cewa ya bi duk wani abu da ya faru a lokacin, saboda haka ne yake kiran da a bi musu hakkinsu.