MDD ta yi kiran a maganta yunwa a duniya
September 24, 2021Talla
Mr. Guterres wanda ya yi kiran samar da daidaiton na abinci a lokacin jawabi a kan abin da ya shafi yaki da yunwa lokacin babban taron MDD da ke ci a birnin New York, ya jaddada bukatar wadatuwar abinci mai inganci da kuma amfani ga mutane a koda yaushe.
Akwai dai mutum biliyan uku ba sa samun abinci mai lafiya a duniya, yayin da ake da mutum miliyan 462 da suka yi matukar ramewa saboda rashin koshi.
Ana hakan ne kuwa a cewar Guterres, ake da mutum biyan biyu a duniyar wadanda suke fama da kiba mai tsanani.
Sai kuma karuwar zubar da abinci a cewar sa a wasu yankuna na duniya da ya kai yawan kashi daya cikin uku na abinci da ake da shi a duniya.