Matakin yaki da yunwa a kasashen tafkin Chadi
February 24, 2017Kasashe 14 sun yi alkawarin samar da dala miliyon 672 don taimakawa kasashen tafkin Chadi da ke kan hadarin fuskantar yunwa a bana, a wani taron kasashe na birnin Osla babban birnin kasar Norway. Kimanin mutane miliyan 11 ne a yankunan Najeriya da Kamaru da Nijer da kuma Chadi da suka fuskanci ibtila'in Boko Haram ne ke cikin wannan matsala. Hukumar agaji ta majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji na Jamus da kuma Najeriya ne suka shirya taron, inda ake neman dala biliyan daya da rabi saboda agazawa kasashen.
Ministan harkokin wajen kasar Norway Borge Brende, ya ce ana bukatar tallafin kasashe masu yawa don samun wadatattun kudade don shawo kan matsalolin da suka bayyana zahiri a yankunan. An dai yi hasashen samun tsananin karancin abinci a yankunan kasashen, inda ko a yanzu ma wasu na matukar kokawa da kasance cikin matsalar. Kungiyoyin agaji da dama ne dai suka tabbatar da ganin manyan alamu na fuskantar yunwar da ake batu kanta.