1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin kasashen duniya kan zaben shugaba Putin

Yusuf Bala Nayaya RGB
March 19, 2018

Wasu daga cikin shugabanin kasashen duniya sun mika sakon taya murna a yayin da wasu ke cewa ba su yi mamakin sakamakon zaben Rasha da ya sake bai wa shugaba Vladimir Putin nasara don yi wa'adi na hudu ba.

https://p.dw.com/p/2uZu9
Russland Wahlen 2018 - Wahlsieg für Putin
Hoto: Reuters/D. Mdzinarishvili

Shugaba Vladimir Putin dan shekaru 65 da ya hau mulkin Rasha kusan tsawon shekaru 20 ya samu gagarumin rinjaye na sama da kashi 76.66 cikin dari na kuri'un da aka kada, sakamakon da ke zama mafi kyau ga Putin, da 'yan adawa ke bayyanashi a matsayin sakamakon rainin hankali da zai sanya kasarsu sake fadawa cikin yanayi na koma bayan tattalin arziki, da kwashe kudin kasar ana harkoki na yake-yake a wasu kasashe, ga yanayi na neman mayar da adawa ta zama mara tasiri. Sai dai a cewar Ksenia Sobchak da ke zama daya cikin 'yan adawa da Putin, rabuwar kai tsakaninsu 'yan adawa ta taka rawa wajen samun nasarar Putin domin Alexei Navalny babban dan adawa ya bayyana ta da zama mai fuska biyu:

Demonstrationen in Wladiwostok Anhänger Navalny
Magoya bayan jam'iyyun adawa sun yi zargin magudi a zabenHoto: picture-alliance/AP Photo/A. Khitrov

Putin ya kara da 'yan takara bakwai ciki kuwa har da babban dan adawa Alexei Navalny da aka haramta wa shiga harkokin na zabe saboda wasu dalilai na shari'a. Mai magana da yawun Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, Steffen Seibert ya ce Merkel za ta taya Putin murna amman wani batu da za ta tabo, shi ne kalubale kan dangantaka a tsakanin Rasha da Jamus kama daga batun Ukraine zuwa yakin da ake yi a Siriya. Shi kuwa Gernot Erler, jami'i da ke lura da harkokin da suka shafi kasar Rasha a gwamnatin Jamus ya bayyana yanayin fitar sakamakon zaben na Rasha a matsayin abu tsararre:

Ya ce a "wannan yanayi da ake ta takkadama da Birtaniya bai zama abin mamaki ba ganin yadda Shugaban na Rasha Vladmir Putin ya sallami jami'an diflomasiya na Birtaniya 23 daf da yin wannan zabe, wannan abu ne da ya kara ba shi dama ya yi yadda ya so har ta kai shi ga yin nasara a zaben."

Russland | Merkel trifft Putin
Shugabar Jamus Angela Merkel ta taya Putin murnar lashe zaben shugaban kasaHoto: picture-alliance/dpa/Sputnik/S. Guneev

Haka ma dai ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, ya na mai ra'ayin cewa batu na a yi zabe mai adalci a zaben na Rasha ma bai taso ba. Ya ce "sakamakon zaben na Rasha ya bamu mamaki ne ta hanyar da aka bi aka yi zaben, abu ne da ba zai yiwuwu ba a ce an yi adalci, kamar yadda muka sani, kuma ma sakamakon da aka bayyana a yankin Crimea lamari ne da ba za a lamunta ba, mun sani cewa Rasha za ta zama kawa mai wuyar sha'ani, zamu ci gaba da tattaunawa da ita amma dole su bada gudunmawa a tafiyar fiye da yadda aka yi a watanni na baya-bayan nan."

Daga yankin Asiya kuwa kasar China bayan da Shugaba Xi Jinping ya taya takwaransa na Rasha murna kamar yadda Shinzo Abe na Japan ya yi, kasar ta Japan dinma bayyanawa ta yi cewa nasarar ta Putin wata dama ce da za ta sanya su sake bude sabbin babi na dangataka da kasar ta Rasha. Yoshihide Suga shi ne sakataren majalisar zartarwar kasar ta Japan ya yi tsokaci.  Ya ce Rasha kasa ce mai muhimmanci ga yankin Asiya da Pacific musamman rawar da take takawa ta fannin tsaro da ci gaba don haka kasashen biyu za su inganta dangantaka da ke tsakaninsu musamman bayan sake zaben na Shugaba Putin. Masu sanya idanu a yayin zabe, sun bayyana zargin magudi a zaben na Rasha da mahukuntan na fadar Kremlin suka yi kokari na ganin ya bai wa Putin dama ta ci gaba da jan ragamar kasar a karo na hudu.