1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaMaroko

Aikin ceto a Marokko na fama da kalubale

Mahmud Yaya Azare LMJ
September 11, 2023

Mazauna yankunan da girgizar kasar da ta afku a Marokko ta shafa, na kin koma wa gidajensu da suka tabu sakamakon girgizar da ta hala dubban mutane.

https://p.dw.com/p/4WDEI
Marokko | Girgizar Kasa | Asarar Rayuka | Kalubale | Aikin Ceto
Adadin wadanda suka halaka a girgizar kasar da ta afku a Marokko na karuwaHoto: FADEL SENNA/AFP

Alkaluman karshe da mahukuntan na Marokko suka fitar na nuni da cewa, kimanin mutane 2,500 ta halaka ban da wasu ninkinsu da suka jikkata. Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da masana ke nuna fargabar amsa amon girgizar kasar ya juyo, lamarin da ya sanya galibin mutanan da nke zaune a yankunan da girgizar kasar ta afku suke ci gaba da kaurace wa gidajensu da zama a fili. Kungiyoyin agaji na kuka a kan rashin samun damar isa kauyukan da girgizar kasar ta yi wa illa, domin kubutar da mutanen da suka makale a karkashin burakuzan gine-gine. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ana bukatar manya-manyan motocin gyaran titi, domin share hanyar isa kauyukan da ke tsananin bukatar agajin.

Marokko | Girgizar Kasa | Asarar Rayuka | Kalubale | Aikin Ceto | Marrakesh
Ma'aikatan agaji na fuskantar kalubale wajen gudanar da aikin ceto a MarokkoHoto: Said Echarif/AA/picture alliance

Tuni dai fadar Masarautar Morokkon ta ayyana makokin kwanaki uku a kasar, domin alhinin wadanda suka mutu. Haka kuma gwamnatin kasar, ta umarci dakarun sojojinta su tallafa wajen kai kayan abinci da magunguna da barguna ga mutane da lamarin ya shafa. Kakakin Majalisar Dinkin Duniya  Farhan Haq ya sanar da cewa, kimanin mutune dubu 300 ne girgizar kasar ta shafa a garin Marrakesh da garuruwan da ke zagaye da shi. Ya kuma bayyna cewa Majalisar Dinkin Duniyar, ta yaba da irin daukin gaggawar da kasashen duniya suka kai. A hannu guda kuma Hukumar Raya Al'adu da Ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO, ta ce za ta taimaka wa Morokko domin sake gina wuraren tarihin kasar da ibtila'in ya shafa. Tsohon birnin Marrakesh wanda girgizar kasar ta shafa sosai dai, na da wuraren tarihi na duniya masu yawa.