Maroko: Ana ci gaba da aikin ceto bayan girgizar kasa
September 10, 2023Girgizar kasa mai karfin gaske ta auku a kasar Maroko, inda kawo yanzu ta yi ajalin mutane sama da 2000. Ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar ta ce iftila'in ya faru ne a ranar Juma'a da daddare, ta kuma ce ta yi nasarar ceto rayukan mutum sama da 2000 da tuni aka kwantar da su a cibiyoyin kiwon lafiya.
Masana sun ce karfin girgizar kasar ya kai zurfin kilomita 18.5 a karkashin kasa. Cikin biranen da abin ya faru akwai al-Haouz da Marrakesh da Azilal da sauransu. Wannan dai ita ce girgizar kasa da a karon farko karfinta ya girgiza hatta biranen Rabat da Casablanca da ke makwabtaka da biranen da ta fi kamari.
Gidaje da yawa sun ruguje, lamarin da ya yi sanadiyyar katsewar wutar lantarki a sassa dabam-daban. Sai dai mahukuntan kasar sun ce girgizar kasar ta fi muni a yankunan karkara da ke nesa da manyan birane.
Shugabannin duniya musamman wadanda ke halartar taron koli na kungiyar kasashe 20 masu karfin tattalin arziki, G20, sun aike wa Sarki Mohammed VI ( na 6) sakon jaje da ta'aziyyarsu ga gwamnatin Maroko a kan wannan al'amari, inda wasu daga cikin shugabannin suka fara kokarin ganin yadda za aike wa da Marokon gudunmawar tallafa wa mutanen kasar gina sabuwar rayuwa.