Mali: Gomman rayuka sun mutu a harin ta'addanci
September 8, 2023Talla
Ana dai zargin 'yan ta'addan da kai mabambanta hare-haren ne kan wani jirgin ruwa a kusa da Timbuktu da kuma sansanin soji da ke Bamba a arewaci yankin Gao.
Hukumomi Mali sun ce harin ya salwantar da rayuwar fararen hula 49 da kuma jami'an soji 15.
Karin bayan:'Yan jihadi sun halaka mutum guda a Timbuktu
A cewar gwamnatin kasar, kungiyar nan ta masu tsattsauurar ra'ayin addini ta JNIM da ke da alaka da al-Qaida ne suka dauki alhakin kai hare-haren.
Tun dai a karshen watan Augustan shekarar 2023 ne kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai suka doshe hanyoyin birnin Timbuktu yayin da rundunar sojin Mali ta tura da dakarunta yankin, inda suka hana kai kayan abinci zuwa birnin da ke a hamadar sahara.