Al-Qaida: Ba mu da hannu a kisan Mali
June 24, 2022A cikin sanarwa da wata kungiya mai zaman kanta ta Amirka ta tabbatar a sahihancinta, Kungiyar da ke da alaka da al-Qaida ta ce ta je yankin Dillassagou ne kawai don neman wadanda suka hada kai da sojojin Mali wajen haddasa mutuwar Musulmi. sai dai gwamnatin Mali ta dora alhakin kisan kiyashin da aka yi a Dillassagou a karshen makon jiya a kan Katiba ta Macina.
Kashe-kashen da aka yi a Dillassagou na daya daga ciki mafi muni da aka yi wa fararen hula a Mali a shekarun baya-bayan nan a yankin Sahel. Sai dai Katiba ta Macina mai tsaurin kishin addini ta yi ikirarin tafiya da wasu da mutane da take zargi, domin gabatar da su a gaban hukumar da ke kula da shara'ar Musulunci.
Kasar Mali ta fada cikin mawuyacin hali na tsaro da siyasa tun bayan barkewar rikicin aware a 2012 a arewacin kasar.