Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yawan ta'adin zafi
July 26, 2024Talla
Wannan gargadi na Antonio Guterres ya zo ne bayan bayyana ranar Litinin da ta gabata a matsayin ranar da ta fi kowacce zafi a tarihi.
Zafin dai a cewar masana ya fi haddasa kisa sama da sauran bala'o'i da sauyin yanayi ke haddasawa, masalan guguwa ko kuma ambaliyar ruwa.
Zafin da ke kisan mummuke, ya yi sanadin mutuwar akalla mutum dubu 489 duk shekara a tsakanin shekara ta 2000 zuwa 2019.
Yayin kuma da guguwa ke kashe rayuka kimanin dubu 16 a kowace shekara a duniya.
Don haka ne ma Majalisar Dinkin Duniya ke kiran da a kara azama wajen rage barnar da zafin ke yi, ta hanyar ankararwa da kuma daukar matakai na sanyaya yanayi gami da kyautata tsara birane da kuma kare masu aiki a filin Allah Ta'ala.