1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaChadi

Mahamat Deby zai yi takarar shugabancin Chadi

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
January 15, 2024

Jam'iyyar MPS ta tsayar da Janar Mahamat Deby Itno takarar shugabancin kasa a zaben karshen shekarar 2024, wannan mataki ya gudana ne a babban taron da ta gudanar a N'Djamena, lamarin da ke nuna cewa zai tube kaki.

https://p.dw.com/p/4bGBy
Shugaban mulkin sojan kasar Chadi Mahamat Idriss Deby
Shugaban mulkin sojan kasar Chadi Mahamat Idriss DebyHoto: DENIS SASSOU GUEIPEUR/AFP/Getty Images

Mahalarta babban taron jam'iyyar MPS sun tsayar da shugaban gwamnatin mulkin sojan Chadi Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin dan takararsu a zaben karshen shekarar 2024. Mai shekaru 37 a duniya  Mahamat Idriss Deby Itno  zai kasance dan takarar jam'iyyar MPS mai matsakaicin shekaru a tarihi, tun bayan mutuwar mahaifinsa a fagen daga a cikin watan Afrilun shekarar 2021.

A karshen shekarar 2023, gwamnatin mulkin soja ta rikon kwarya da Mahamat Idriss Deby ke jagoranta, ta yi nasarar samar da sabon kundin tsarin mulki, bayan da 'yan kasar suka kada masa kuri'ar yin na'am da gagarumin rinjaye.

Karin Bayani : Chadi: Shirin zaben raba gardama kan kudin tsarin mulki

A farkon wannan shekarar, gwamnatin Mahamat Deby ta nada jagoran 'yan adawa Succès Masra a matsayin firaministan kasa, wanda ya yi alkawarin aiwatar da wasu muhimman sauye-sauyen da suka dace don karfafa dimukuradiyya da ci-gaban kasar.

Jam'iyyar MPS ta marigayi Idriss Daby, ta share shekaru akalla 30 tana mulki a Chadi, sojoji sun nada gwamnatin rikon kwarya a karkashin Mahamat Idriss Deby a matsayin wanda ya gaji mahaifinsa da ya mutu a fagen yaki da 'yan tawaye.