1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kungiyar NLC a Najeriya ta jingine yajin aiki

February 28, 2024

A daidai lokacin da gamayyar kungiyoyin kwadagon Najeriya suka tsunduma yajin aikin gama-gari, sakamakon tsadar rayuwa, jaridun Najeriya sun rawaito cewa kungiyar ta NLC ta jingine yajin aikin tare da jaddada nasara.

https://p.dw.com/p/4cxsk
Zanga-zangar NLC a Abuja Najeriya
Zanga-zangar NLC a Abuja NajeriyaHoto: Uwais/DW

Shugaban kungiyar Joe Ajaero, shi ne ya tabbatar da dakatar da shiga rana ta biyu da zanga-zangar ga jaridun Najeriya, tare da nuna takaicinsa kan yadda gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma da kuma magance matsalar tsadar rayuwa da hauhawan farashi da ya dabaibaye al'ummar Najeriya.

Karin bayani:Najeriya: Kungiyar NLC ta yi watsi da karin farashin mai

Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya hau kan karagar mulkin kasar a 2023, shi ne ya bujiro da wasu tsare-tsare da suka hadar da janye tallafin man fetur da yin garambawul kan tsarin musayar kudi, da hakan ya haifar da faduwar darajar Naira kan Dalar Amurka a kasuwannin musayar kudaden kasar.

Karin bayani:Yajin aikin gargadi a Tarayyar Najeriya