Najeriya: Tinubu a komar 'yan kodago
September 5, 2023Shugabannin kungiyar Kodagon NLC reshen Abuja babban birnin Tarayyar Najeriyar, sun yi ta korar ma'aikata zuwa gida a ma'aikatar kudi. Kama daga ofisoshin gwamnati zuwa ga bankuna da ma ma'aikatan wutar lantarki, kungiyoyi da daman gaske sun shiga yajin aikin na gargadi da ke da zummar aike sako kan wahalar da ma'aikatan suke ikirarin zare tallafin man fetur ya haifar. Duk da cewar dai babu alamun gurgurcewar harkoki a cikin birnin da mazaunansa ke hada-hada kamar ko yaushe, masu kodagon da suka yi fatali da rokon 'yan mulkin kasar sun yi nasarar gurgunta ayyukan hukuma. Kwanaki 100 bayan zare tallafin man fetur dai, ma'aikatan gwamnatin tarayyar na zaman jiran cikon alkawarin gwamnatin kan rage radadin matakin da ya janyo tashin gauron zabi na daukacin kayan bukatun rayuwa.
Fatan rangwamen karuwar azaba ko kuma hutun jaki da ke da kaya kansa dai, 'yan kodagon sun rika bi ofis-ofis suna tilasta ma'aikata barin aikin domin zuwa gida. Abun da ke nuna alamun rabuwar kai, tsakanin 'yan kodagon da ragowar ma'aikatan da ke tunanin aikin zaki. Kwamared Mohammed Gambo dai na zaman mai binciken kudi na kungiyar ta NLC reshen Abujar, ya kuma ya zargi masu mulkin Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da murde wuyan ma'aikata. Koma ya zuwa ina dabarar 'yan kodagon ke iya kai wa a cikin aiken sako ga gwamnatim dai, kan ma'aikatan na rabe dangane da yajin aikin a cikin halin babu. Wani ma'aikacin da ya nemi a boye sunansa dai, ya ce matakin NLC na kama da yin bulala ga mattacen jaki. Ma'aikatar kodagon kasar dai ta ce nan da makonni biyun da ke tafe ne, Abujar ke fatan fara samar da tallafin rage radadin ga ma'aikatan da ke fadin wayyo Allah yanzu.