1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Yajin aikin gama-gari ya tsayar da lamura a Najeriya

Uwais Abubakar Idris ZMA
June 3, 2024

Yajin aikin na zuwa ne bayan gaza cimma matsaya kan mafi karancin albashin ma'aikata tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da kungiyar kwadago NLC.

https://p.dw.com/p/4gZM2
Hoto: Uwais/DW

Al’amura sun tsaya cik a ma’aikatun gwamnatin Najeriya bankuna da ma wasu wuraren kasuwanci sakamakon yajin aiki na gama-gari da kungiyar kwadagon Najeriyar ta fara a kasar a kan gwamnati ta kara masu albashi mafi kankanata daga Naira dubu 30 zuwa dubu 494. 

Tun 12 na daren Litinin ne 'ya'yan kungiyar kwadago suka fara da katse kusan daukacin manyan injinan bada wutan lantaraki a Najeriya a mataki na nuna da gaske suke a kan wannan yajin aiki na gama-gari, wanda suka daka suke sha abinsu biyo bayan watsewa baram-baram a kokarin da shugabanin majalisar dokokin kasar suka yi na shawo kan 'yan kwadagon.

Manyan kungiyoyin kwadagon kasar biyu na TUC da NLC da ke jagorantar daukacin kungiyoyin kwadagon kasar ne suka yi watsi da tayin albashi mafi kankanta na Naira dubu 60 da gwamnati ta yi musu, inda suka dage lallai sai ya kai Naira dubu 494. Anya suna ganin abu ne mai yiwuwa? 

Nigeria Protest NLC Abuja
Hoto: Uwais/DW

Na zagaya cikin birnin Abuja da kewaye inda na iske mafi yawan bankuna 'yan kwadagon sun tilasta musu sun rufe, haka nan ofishin gwamnati ma fayau, hatta tashar jiragen sama ta Abuja na iske fasinjoji sun yi cirko-cirko don an hana jiragen sama sauka ko tashi. Akwai ‘yan Najeriyan da ke nuna adawa da yajin aikin sanin halin da al'ummar kasar ke ciki a yanzu. 

Gwamnatin Najeriyar dai ta ayyana yajin aikin a matsayin haramtacce inda ta yi barazana ga 'yan kwadagon a kan fuskatar daurin watanni shida domin sashi na 18 na dokar 'yan kwadago ya nemi ma’aikatan da ke gudanar da muhimman aiyuka su bada sanarwar kwanaki 15 kafin su fara yajin aiki.

Nigeria | NLC Protest
Hoto: Nasir Salisu Zango

Kwararru na bayyana koma bayan da yajin aiki ke haifarawa ga gwamnati da ma sauran al'umma musamman yadda ya gurgunta harkar samar da wutan lantarki, bankuna dama zirga zirga jiragen sama.