Kotun ICC za ta yanke hukunci kan masu Ikrarin jihadi a Mali
April 16, 2024Babban mai shigar da kara na kotun ICC ya ce mutanen ciki har da Al Hassan wanda ya yi kaurin suna wajen azabtar da mutane da yiwa mata fyade da bautar da su harma da yi musu auren dole ga 'ya'yan kungiyar ta masu ikrarin jihadi a yankin Timbuktu da ke kasar ta Mali.
Karin bayani: Tsageru suna kara kaimi a Mali
Al Hassan shi ne mutum na biyu daga cikin masu ikrarin jihadin da aka gabatar a kotun ICC kan zargin lalata wasu muhimman wurare na addini da na tarihi da hukumar UNESCO ta ware a matsayin wurare masu matukar muhimmanci.
Karin bayani: ICC: Al Faqi zai biya diyyar hubbaren Timbuktu
Kotun dai ta yanke wa mutum na farko Ahmad Al Faqi Al Mahdi hukuncin daurin shekaru 9 a shekara ta 2016, wanda bayan daukaka kara kotun ta rage daurin zuwa shekara 2 a 2021.