1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali tana rasa sassan kasar

Suleiman Babayo ZMA
September 27, 2023

Sojojin da suka kwace madafun ikon kasar Mali suna ci gaba da rasa wasu sassan kasar sakamakon kungiyoyin jihadi da suka katse hanyoyin zuwa birnin Timbuktu da kewaye na arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/4WqZx
Mali - Timbuktu
Birnin Timbuktu na arewacin maliHoto: dpa

Kungiyoyin da ke ikirarin jihadi na kasar Mali sun katse hanyoyin da ke kai wa zuwa birnin Tumbuktu da kewaye na arewacin kasar, abin da ya jefa dubban mutane mazauna yankin cikin yanayin tararrabi da tashin farashin kayayyaki.

Tun farko kungoyoyin masu nasaba da al-Ka'ida sun saki sakon barazanar karbe iko da hanyoyin da ke kai wa yankin tare da cewa duk wata motar daukan kaya da ta kutsa yankin za su kona. Kana hanyar zuwa yankin ta ruwa an daina bi sakamakon yadda fararen hula suka halaka lokacin da tsagerun suka kai hari kan kananan jiragen ruwa na fasinja.

Birnin na Timbuktu da ke arewacin kasar ta Mali da sauran yankunan da ke zagaye da shi sun fara shiga rudani sakamakon matakin janye dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, ita kanta gwamnatin mulkin sojan kasar ta Mali da ke yankin yammacin Afirka, wadda ta kwace madafun iko tun shekara ta 2020 kuma ta bukaci janye dakarun na kasashen duniya, ta fito fili yanzu ta ce tana fuskantar gagarumin kalubalen tsaro da ke kawo tarnaki wajen jigilar kayayyakin bukatun rayuwa.