1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta koma cibiyar gwajin makamai

March 6, 2019

Koriya ta Arewa ta koma cibiyar da ta rusa a bara bayan da hukumomin Amirka suka nuna na jingine batun manyan makaman da take tayar da hankalin duniya da su.

https://p.dw.com/p/3EY1t
Nordkorea Raketentest auf Startanlage Sohae
Hoto: picture-alliance/Yonhap

Hukumomin birnin Pyonyang, sun koma aiki gadan-gadan a cibiyar nan nasu ta harbe-harben manyan makamai, cibiyar da ta rusa a bara cikin wani shirin kwance damarar yaki.

Wannan labarin wanda ya fito daga jami'an leken asiri gami da wasu kwararru daga kasashen wajen Koriyar, na zuwa ne bayan ganawar da Shugaba Kim Jong Un ya yi da takwarsa na Amirka Donald Trump a makon jiya ba tare da kaiwa ga wata matsaya ba.

A makon na jiya kasashen biyu sun tashi ne suna zargin juna a kan abin da ya hana su cimma yarjejeniya a ganawarsu ta birnin Hanoi na kasar Vietnam.

Ya zuwa yanzu dai Koriyar ba ta ce komai dangane da sake bude cibiyar da ta yi ba.