Koriya ta Arewa za ta daina gwajin makamai
April 29, 2018Shugaba Kim Jong Un na kasar Koriya ta Arewa, ya ce zai rufe cibiyar nan ta gwaje-gwajen makaman Nukiliya a kasarsa, cikin watan gobe na Mayu mai shirin kamawa. Mr. Kim wanda ya fadi hakan a ziyararsa ta tarihi a kasar Koriya ta Kudu, ya yi alkawarin gayyatar kwararru daga Amirka da Koriya ta Kudu da 'yan jarida don ganin yanda za a rufe cibiyar.
Yayin ziyarar ta Juma'a dai, shugabannin Koriyoyin biyu, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar daina amfani da makaman Nukiliya a yankin nasu, abin kuma da zai kawo karshen gardama tsakaninsu. Tun cikin shekarun 1950 ne dai ake ta ja-in-ja tsakanin Koriyoyin biyu, ba tare da wani shiri na sulhu a tsakani ba.
Wasu masana kimiyya 'yan kasar China dai sun ce cibiyar ta lalace, a gwajin baya-bayan nan da Koriya ta Arewar ta yi, sai dai fa wasu jami'an leken asirin Amirka sun ce wajen na aiki.