1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karshen taron G20 a birnin Hamburg

July 8, 2017

A wannan Asabar ne aka kammala taron kolin kasashe 20 masu cigaban masana'antu na G20 da aka yi a birnin Hamburg na nan Jamus.

https://p.dw.com/p/2gD8n
Deutschland, Hamburg, G20 Proteste
Hoto: Getty Images/AFP/P. Stollarz

A jawabin da ta yi a bayan taron shugabar gwamnati Angela Merkel ta bayyana cewa daukacin kasashen 20 sun amince da matakan daidaita kasuwar hada hadar kudade da yaki da ta'addanci da kuma yakar halayyar kaucewa biyan haraji, wadanda suna daga cikin dalilan da suka jefa duniya cikin matsalar hada hadar kudade a shekarar 2008.

Shugabar gwamnatin ta Jamus Angela Merkel ta kuma nuna bacin rai kan zanga zangar da ta rikide zuwa tarzomar adawa da wasu manufofin taron, tana mai danganta wadanda suka aikata hakan da marasa kishin dimokradiyya.

'Yan sanda kimanin dubu ashirin daga nan Jamus da kuma wasu kasashen turai suka bada kariya wajen tabbatar da tsare zanga-zangar.