Jam'iyyar PDP ta fusata a Najeriya
January 26, 2019A Najeriya, babbar jam'iyyar adawar kasar wato PDP, ta sanar da dakatar da yakin neman zabenta na tsawon kwanaki uku, domin bayyana fushinta kan matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na dakatar da alkalin alkalan kasar a ranar Juma'a.
Shugaban kasar ya dakatar da Justice Walter Onnoghen ne, wanda ke gaban kotu kan zargin taka dokokin da suka danganci bayyana gaskiyar kadarorin da ya mallaka.
Lauyoyin babban alkalin sun ce kotu ba ta da ikon gabatar da shi kan wannan batun.
Fannin shari'ar Najeriyar dai na taka rawa kan rigingimun zabe, musamman inda ake zargin tafka magudi, aikin kuma da ake ganin Justice Onnoghen ka iya yi bayan babban zaben kasar na watan gobe da tuni aka yi hasashen yiwuwar samun magudin.
Jam'iyyar PDPn na fatan Shugaba Buhari, zai saurari muryar masu kaunar dimukuradiyya da ma ta al'umar duniya wajen kauce wa galatsi ga doka.