1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jagoran Hamas Ismail Haniyeh ya isa Masar kan rikicin Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 20, 2024

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da bukatar da Hamas ta mika ta tsagaita wuta nan take, ficewar Isra'ila daga Gaza, da kuma bude hanyoyin zirga-zirga

https://p.dw.com/p/4ccSe
Hoto: Fazil Abd Erahim/AA/picture alliance

Jagoran kungiyar Hamas Ismail Haniyeh ya isa birnin Alkahira a Talatar nan, don tattaunawa da gwamnatin kasar Masar kan hanyoyin bi don kawo karshen rikicin Gaza.

Karin bayani:An gaza cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza

Ko da yake alamu sun nuna cewa Isra'ila za ta ci gaba da abin da ta kira kawo karshen kungiyar Hamas da kasashen yamma suka ayyana a matsayin ta ta'addanci.

Karin bayani:Isra'ila na shan suka kan farmakin da ta kai Rafah

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da duk wata bukata da Hamas ta mika don samun masalahar rikicin, bayan da Hamas din ta bukaci tsagaita wuta nan take, ficewar dakarun Isra'ila daga Gaza, da kuma bude hanyoyin da Isra'ilan ta jima da datsewa don bai wa Falasdinawan damar zirga-zirga.