1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gaza cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

February 18, 2024

Firanministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya bayyana bukatun kungiyar Hamas a tattaunawar zaman lafiya a birnin Alkahiran Masar a matsayin mara tabbas.

https://p.dw.com/p/4cXYs
An gaza cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza
An gaza cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a GazaHoto: Mohammed Salem/REUTERS

Bukatun dai sun hada da kawo karshen yakin ta hanyar janyewar Isra'ila gaba daya daga yankin, da barin kungiyar ta Hamas a yadda take. Kungiyar ta kuma bukaci a saki dubban Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila, fursononin da Netanyahu ya bayyana su a matsayin masu kisan kai.

Sai dai shugaban kungiyar ta Hamas, Ismail Haniyeh ya daura alhakin rashin samun ci gaba a tattaunawar a kan Isra'ila a yayin da Masar da kuma Qatar ke shiga tsakani domin ganin an cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a rikicin Zirin Gaza.

Haniyeh ya kuma ce Hamas ba za ta amince da ragi daga bukatunta ba.