Kwamandan Isra'ila na cikin dakaru 10 da suka mutu a Gaza
December 13, 2023Wani babban kwamandan sojojin Isra'ila Kanar na cikin dakaru 10 da kasar ta yi asara yayin fafatawa da mayan kungiyar Hamas a Talatar nan (12.12.2023), kamar yadda rundunar sojin ta sanar.
Karin bayani:Jakadun MDD sun kadu da abin da suka gani a Rafah
Isra'ilar dai na ci gaba da fuskantar matsin lambar tsagaita wuta kan luguden bama-baman da take ci gaba da yi wa yankin Zirin Gaza na Falasdinu, bayan da babban zauren Majalisar Dinkin Duniya mai mambobi 193 ya amince da kudurin tsagaita wuta, wanda bai samu goyon bayan Amurka da Isra'Ila da kuma wasu kasashe 8 ba.
Karin bayani:Kasashen larabawa na yajin aiki kan Gaza
A gefe guda kuma wasu faya-fayan bidiyo da hotuna sun nuna sojojin Isra'ila suna shiga gidaje da shagunan jama'a suna lalata kayan abinci da ruwan sha da ma duk wani abu mai amfani da suka ci karo da shi, inda suke rawa suna waka a Gaza.
Ko da yake rundunar sojin Isra'ilar ta sha alwashin daukar matakin ladaftarwa ga sojojin da aka samu da aikata hakan.