Jakadun MDD sun kadu da abin da suka gani a Rafah
December 11, 2023Jakadun kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun baiyana matukar damuwa game da halin tagaiyarar al'umma a Gaza. Jakadun sun baiyana hakan ne yayin ziyarar da suka kai mashigin Rafah da ke iyaka da kudancin Gaza
Ziyarar na zuwa yan kwanaki bayan da Amurka ta hau kan kujerar na ki kan kudirin Majalisar Dinkin Duniya na neman tsagaita wuta.
Ziyarar ta kwana guda kasar Hadaddiyar daular laraba da kuma Masar suka shiryata yayin da ake ci gaba da fuskantar matsanancin halin rayuwar al'umma a Gaza da yaki ya daidaita, yankin da sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya baiyana da cewa ya zama tamkar makabarta.
Jakadu daga kasashe da dama da suka hada da Rasha da Birtaniya na daga cikin ayarin da suka kai ziyarar. Sai dai Amurka wadda ta hau kujerar na ki akan kudirin tsagaita ba ta tura wakili ba a ziyarar haka ma kasar Faransa.
Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Masar ya shaidawa jakadun cewa babu wata hujja da za ta sa a kau da kai daga ukubar da ake gana wa al'ummar Falasdinawa a Gaza.