Isra'ila ta saki wasu fursunonin Falasdinu
April 15, 2024Hukumomin Gaza sun sanar da cewa Isra'ila ta saki Falasdinawa fuursuna akalla 150 a ranar Litinin 15.04.2024, sai dai amma sun ce an azabtar da fursunonin a lokacin da ake tsare da su.
Wani kusa a gwamnatin Hamas ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa an garzaya da dama daga cikin fursunonin zuwa asibin Abu Yusef al-Najjar domin kula da lafiyarsu.
Karin bayani: Shirin wata sabuwar yarjejeniya tsakanin Isra'ila da Hamas
Sai dai dakarun Isra'ila ba su ce uffan ba a game da sakin wadannan fursunoni da ake zargin sun azabtar a lokacin da suke tsare da su.
Wasu majiyoyi sun bayar da rahoton cewa an taso kyeyar fursunonin zuwa yankin Falasdinu daga mashigar kudanci Gaza ta Karem Shalom da ke iyaka da Isra'ila.
Karin bayani: Isra'ila ta bude sabuwar hanyar isar da kayan agaji Gaza
A watan da ya shige shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta yankin Falasdinu Philippe Lazzarini, ya bayyana damuwa a game da halin da fursunonin da Isra'ila ta tsare ke ciki, yana mai cewa dama da aka sallama su dawo gida ba sa cikin hayyacinsu.