1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta bude sabuwar hanyar isar da kayan agaji Gaza

April 12, 2024

Isra'ila ta sanar da bude wata sabuwar hanya domin shigar da kayan agaji daga Kudancin zirin Gaza inda tuni ayerin tireloli na farko shake da kayan abinci ya isa yankin na Falasdinu da yaki ya daidaita.

https://p.dw.com/p/4eiGx
Isra'ila ta buda sabuwar hanyar isar da kayan agaji Gaza
Isra'ila ta buda sabuwar hanyar isar da kayan agaji GazaHoto: Israeli Army via AFP

A cikin wani faifan bidiyo da ya biyo bayan wannan sanarwa, an nuna yadda tun a ranar Alhamis 11.04.2024 motocin farko shake da kayan agaji suka fara shiga Gaza bisa sa'idon sojojin Isra'ila bayan kwakkwaran bincike.

Sai dai har kawo wannan lokaci Isra'ilar ba ta bayar da cikakken bayani ba kan adadin motocin da suka isa zirin na Gaza sannan kuma ba ta yi karin haske ba kan bangaren da aka buda wannan sabuwar hanya.

Wannan mataki na zuwa ne bayan share tsawon watanni kasashen duniya cikin har da Amurka suna rarrashin Isra'ila kan buda hanyoyi domin ba da damar kai dauki ga al'ummar Falasdinu da suka fara fuskantar bala'in yunwa.