1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSaudiyya

Isra'ila da Saudiyya na daf da dinkewa

September 23, 2023

A wani abu mai kama da kyautata alaka a tsakanin kasashen Isra'ila da Saudiyya, kasashen biyu na nuna alamu na rungumar zaman lafiya a tsakninsu a baya-bayan nan.

https://p.dw.com/p/4Wjnf
Tutocin kasashen Isra'ila da Saudiyya
Tutocin kasashen Isra'ila da Saudiyya

Isra'ila ta aike wa Saudiyya sakon tayin murna a wannan Asabar din da take bikin ranar hadin kan kasa.

Wannan tayin murna na Isra'ila ya zo ne lokacin da kasashen biyu ke kokarin dawo da dangantaka a tsakaninsu.

Ko a jiya Juma'a ma dai Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fada a taron Majalisar Dinkin Duniya cewa suna gab da kafa tarihin zaman lafiya tsakaninsu da Saudiyyar.

Sannan shi ma Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya Mohammad Bin Salman, ya fada wa tashar talabijin din Fox cewa kasashen biyu sun kama hanyar dawo da dangantaka a tsakaninsu.

A shekara ta 2020 ma dai kasashen Larabawa irin su Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa, sun dawo da huldarsu da Isra'ila karkashin wata yarjejeniya, sai dai Saudiyya ta bijire a lokacin.