1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas: Neman a matsawa Isra'ila amincewa da bukatocinsu

Binta Aliyu Zurmi
June 13, 2024

Shugabannin kungiyar Hamas sun yi kira ga mahukuntan Washington da su kara matsawa Isra'ila ta amince da bukatunsu na kawo karshen yakin Gaza gabaki dayansa.

https://p.dw.com/p/4gyhQ
Katar Doha | Hamas-Führer Ismail Haniyeh und Dschihad-Führer Ziad Al-Nakhlej
Hoto: HAMAS MEDIA OFFICE/REUTERS

Wannan kira na Hamas na zuwa ne a yayin da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ke karkare ziyarasa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kungiyar ta Hamas ta ce ta ji yadda Blinken ke magana a kan sabon kudirin yarjejeniyar da suka gabatar amma har yanzu basu ji komai daga bangaren Isra'ilaba.

Sakatare Blinken ya ce wasu daga cikin bukatun na Hamas za a iya amincewa da su amma dai masu shiga tsakani na kokarin ganin yadda za a cimma kyakyawar yarjejeniya.

Daga cikin sauye-sauyen da Hamas ta gabatar akwai bukatar sakin wasu Falasdinawa 100 da ke fuskantar zama kaso na shekaru a gidajen yarin Isra'ila.