1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Halin da ake ciki a siyasar Gambiya

January 20, 2017

Shugaba Yahya Jammeh mai barin gado, ya sanar da cewa a kara masa wa'adin wasu sa'o'i domin ya sauka daga kan karagar mulkin Gambiya.

https://p.dw.com/p/2W7kd
Shugaban kasar Gambiya mai barin gado Yahya Jammeh
Shugaban kasar Gambiya mai barin gado Yahya Jammeh Hoto: Reuters/T. Gouegnon

A wani mataki da za a iya bayyana wa da samun ci gaba, Shugaban kasar Gambiya mai barin gado Yahya Jammeh ya bukaci da a bashi zuwa karfe hudu na ranar Jumma'a 20 ga watan Janairu da muke ciki, domin ya sauka ya kuma mika mulki ga sabon shugaban kasar Adama Barrow. Tunda fari dai shugaban kungiyar ECOWAS Marcel Alain de Souza ya sanar da shirin tumbuke Jammeh da karfin soja, muddin yaki sauka da tsakar ranar ta wannan Juma'a.

Shugabannin kasashen Guinea da Muritaniya sun isa kasar ta Gambiya, domin tattaunawa da Shugaba Yahya Jammeh mai barin gado gabanin cikar wa'adin tsakiyar wannan rana ta Jumma'a 20 ga wannan wata na Janairu da muke ciki, da aka debar masa a matsayin wa'adin barin kan karagar mulkin kasar ko kuma ya fuskanci mataki na soji. Rahotanni sun nunar da cewa tuni dakarun hadakar kasashen yammacin Afirka suka shiga kasar ta Gambiya, yayin da aka ga wasu karin motocin mayaka 20 na kutsawa Gambiyar ta kan iyakar garin Karang. Sojojin kasashen musamman Najeriya da Senegal da Ghana da Mali dama Togo ne suka soma isa Gambiyar jim kadan da aka rantsar da Shugaba Adama Barrow a ranar Alhamis 19 ga watan na Janairu da muke ciki a ofishin jakadancin Gambiya da ke Dakar babban birnin kasar Senegal.