Neman mafitar sulhunta rikicin Habasha
December 21, 2021Gwamnatin Habashan dai ta yi watsi da ikirarin mayakan Tigrya, na cewa sun janye dakarunsu daga yankunan Amhara da Afar bisa radin kansu. Mai magana da yawun gwamnatin ta Habasha Billene Seyoum ta ce mayakan na TPLF sun janye ne, bayan nasarar da sojojin gwamnati suka samu na kakkabe su.
Karin Byani: Rikicin Habasha ya rincabe
Kjetil Tronvoll dan kasar Norwayy ne da ke bincike kan rikici da zaman lafiya a kasashen da ke gabashin Afirka, ya shaidawa DW cewa shigar Firaiminista Aby Ahmed sahun gaba a fagen daga na nuni da kololuwar kishin kasa kuma yadda aka shirya rundunar sojojin ya ba su karfi sosai. A cewarsa hakan ya karya lagon mayakan TPLF yadda ba za su iya ci gaba da mamaye yankuna ba, kana a gefe guda akwai tawaga ta musamman da ke kokarin shawo kan matsalolin ta sigar diflomasiyya.
Kungiyar mayakan yankin na Tigray TPLF dai sun sanar cewa dakarunsu sun janye daga yankin Amhara da kuma Afar, inda suka ce matakin da suka dauka zai bude kofar sulhu. Sun kuma rubutawa Majalisar Dinkin Duniya wasika kan wasu jerin bukatunsu, matakin da gwamnatin Amirka ke fatan zai zamo hanyar tattaunawar diflomasiyya domin kawo karshen rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama.
Karin Byani: Rikicin 'yan aware ya ta'azzara a Afirka
To sai dai ganin yadda bangarorin gwamnati da na 'yan twayen ke ikirarin nasara kan juna, masanin rikicin yankin gabashin Afirkan Kjetil Tronvoll na birnin Oslo a kasar Norway, ya ce ya yi wuri a iya hasashen ko lokaci ne na fara murnan samun zaman lafiya a arewacin aksar. Kusan mutane 60,000 ne suka tsere gudun hijira zuwa kasashe makwabta, sakamakon yakin da aka kwashe watanni 13 ana gwabzawa tsakanin sojojin gwamnatin Habashan da mayakan yankin Tigray da ke arewacin kasar. Habasha dai na zaman kasa ta biyu mafi yawan al'umma a Afirka, kasar da a yanzu yaki ya kassara ta sosai.