Girgizar kasa a Vanuatu ta halaka mutane da rusa gidaje
December 17, 2024Girgizar kasa mai karfin maki 7.3 a ma'aunin richter ta halaka mutane a tsibirin Vanuatu da kewaye a yankin pacific, ciki har da New Caledonia da ke karkashin ikon Faransa, tare da rusa gidaje masu tarin yawa da haddasa zaftarewar kasa a wannan Talata.
Karin bayani:Girgizar kasa ta hallaka mutane 118 a China
Wasu fayafayan bidiyo da hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta na zamani, sun nuna yadda gawarwaki suke a yashe a babban birnin kasar Port Vila, da gadojin da suka karye da baraguzan gine-gine, cikinsu har da ofisoshin jakadancin kasashen Amurka da Faransa.
Karin bayani:Girgizar kasa kasar Philippines ta hallaka mutane biyu
Tuni dai hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar New Zealand da kuma cibiyar nazarin harkokin kimiyya ta GNS suka kaddamar da binciken gano ko akwai alamun faruwar ibtila'in tsunami, to amma babu wani karin haske daga hukumomin Vanuatu kan wannan lamari.