SiyasaAsiya
Girgizar kasa kasar Philippines ta hallaka mutane biyu
December 4, 2023Talla
Girgizar kasa da ta faru daga tsakar daren jiya Lahadi zuwa asubahin yau Litinin a Kudancin kasar Philippines, ta hallaka mutane biyu tare da raunata wasu da dama, kamar yadda hukumar kula da yanayin kasa ta Amurka ta sanar.
Karin bayani:China da Philippines na nuna wa juna dan yatsa
Girgizar kasar ta yi tafiyar Kilomita 72 a yankin Hinatuan na tsibirin Mindanao, kuma ta fara ne tun ranar Asabar zuwa jiya Lahadi har zuwa yau Litinin, in da ta fara nuna alamar tayar da igiyar ruwan Tsunami.
Karin bayani:Biden zai gana da shugaban Philippines
Gine-gine da rufin gidaje sun rushe, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta sanar.