Shirye-shiryen babban zabe a Ghana
December 4, 2020Ofishin babban limamin limaman Ghana da majalisar zaman lafiya ta kasar ne, suka jagoranci yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanya hannun kanta,gabanin babban zaben kasar. Tun daga shekara ta 1992, Ghana ta gudanar da zabubbuka bakwai tare da mika mulki cikin lumana. Ta kuma saurari kararraki na tashe-tashen hankalin siyasa a nahiyar, duk da haka kasar na fatan ci gaba da kare mutuncinta a bangaren wanzar da zaman lafiya da kafa dimukuradiyya a nahiyar, kuma majalisar zaman lafiya ta kasar ta yi imanin hakan zai dore.
Karin bayani: 'Yan aware sun kai hari kan motocin sufuri mallakin gwamnati
A bangaren hukumar zabe mai zaman kanta kuwa, Madam Jean Mensah ta sha alwashin fitar da sakamakon zabe cikin sa'o'i 24 bayan kammala kada kuri'a tare da tabbatar da zaman lafiya: "A karon farko cikin tarihi mun aika da baki dayan takardun zabe zuwa dukkan mazabu domin kada muyi aiki cikin kunci. A daya hannun kuma munyi tanadi sosai a bangare na'urorin aiki, tare da horrar da ma'aikatanmu. Na yi imani zamu cimma buri."
Karin bayani: 'Yan aware na da'awar kafa kasa a Ghana
Su kuwa shugabanin biyu wato tsohon shugaban kasar John Mahama da shugaba mai ci yanzu Akufo-Addo sun sha alwashin tabbatar da zaman lafiya, yayin zaben da ma bayan kammala shi. Tsohuwar shugabar Liberia Hellen Johnson Sirleaf da wakilin musamman na sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya a yankin yammacin Afirka da Sahel kuma shugaban UNOWAS, Mohammed Ibn Chambas sun mika sakonninsu dangane da muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da guje wa tashe-tashen hankula.