1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan aware na da'awar kafa sabuwar kasa a Ghana

September 25, 2020

Wani atisayen hadin gwuiwa tsakanin rundunar soji da ta 'yan sanda a Ghana ya sake karbo ikon yanki Volta awowi kalilan bayan masu rajin kafa kasar Togoland suka karbe iko da yankin.

https://p.dw.com/p/3j162
Ghana Volta Region
Hoto: Elvis Washington

Ayyukan 'yan a ware na kara yin kamari a yankin yammacin nahiyar Afrika kama tun daga masu neman kafa Biafara a Najeriya zuwa ga 'yan Ambazoni da ke neman ballewa daga Jamhuriyar Kamaru, sai kuma na baya bayan nan da ke neman ballewa daga kasar Ghana da niyar kafa kasar Togoland, masu rajin kafa kasar ta Togoland da ke kokarin ballewa daga kasar Ghana sun kafa shingaye a manyan titunan yankin tare da karbe ikon manyan ofisoshin 'yan sandan yankin guda biyu, bayan da suka fasa wani runbun ajiyar makamai inda suka yi awon gaba da bindigogi masu tarin yawa.
 Jami'an 'yan sanda uku ne dakarun 'yan awaren na Togoland ke tsare dasu, wani mazaunin yankin da ke gabashin Ghanar Lambert ya shaidawa gidan radiyon DW halin da suke ciki na fargaba inda ya ce ''Yanzu haka muna cikin wani mawuyacin hali na tsaro, dama tun a 'yan makanin da suka gabata ne muka ga 'yan awaren na lika alamun ballewar a tituna da ke yi wa matafiya barka da zuwa da sunan sabuwar kasar Togoland." Kimanin dakaru dari biyar ne suka samu horon soji a sirrance da baiyana sabuwar tutar kasar Togoland, a wani bangare na kokarin mallakar 'yancin kai wanda hukumomin kasar Ghana suka ce wannan yunkurin ya sabawa dokokin kasar in ji Kobena Woyom wani dan majalisa yana mai cewa ''A matsayina na mai yin dokoki bai kamata ace nine ke baiwa mutane shawara su taka dokokin kasa ba hakan bai dace ba, amma idan wasu suna da korafe-korafe dole a sauraresu." 'Yan a waren sun jima suna yunkuri baiyanar da aniyar tasu ta ballewa daga kasar Ghana domin kafa sabuwar kasar Togoland da zata debo wani bangare na kasashen Togo da Ghana. Kasar Jamus dai ita ce ta fara gudanar da mulkin mallaka a yankin na Togoland kamin daga bisani yakin duniya na daya kasashen Birtaniya da Faransa suka karbe iko da yankin.

Ghana Volta Region
Hoto: Elvis Washington