Côte d' Ivoire: Ganawar Ouattara da Gbagbo
July 27, 2021Wannan dai ita ce ganawa ta farko tsakanin shugaba Alassane Ouattara na Côte d' Ivoire da wanda ya gabace shi, tun bayan da kotun ICC ta wanke Laurent Gbagbo daga zargin cin zarafin dan Adam, lamarin da ya sa shi komawa gida a watan Yunin da ya gabata. Ganawar na zuwa ne, a daidai lokacin da kungiyoyi masu zaman kansu ke kokarin kyautata zamantakewar al'ummar kasar da ta lalace sakamakon salwantar rayuka da dukiyoyi a tashin hankalin. Rikicin da ya biyo bayan zaben shekarar 2010 a Côte d' Ivoire, ya haifar da zaman dar-dar tsakanin al'ummomin arewaci inda Ouattara ke da magoya baya da kudanci inda Laurent Gbagbo ke samun karbuwa. Anastasie Adjoua Kouadja 'yar asalin kudancin Côte d' Ivoire ta yi zaman arziki da Cissé Makoko da ta fito daga arewaci a kauyen Bodoukro da ke da nisan kilomita 120 daga Abidjan.
Karin Bayani: ICC ta wanke Laurent Gbagbo
Rikicin bayan zabe a shekara ta 2010 ya sa bangarorin biyu sun shiga takun saka tsakaninsu, lamarin da ya haddasa asarar rayuka da lalacewar gidaje da gonaki. Sai dai a yanzu Adjoua Kouadja ta yi nadamar wannan tashin hankalin da ya lalata wani bangare na zaman tare. Tun bayan fadace-fadacen da suka salwantar da rayukan mutane 3000, Cissé Makoko da iyalinta suka koma da zama a arewacin Côte d' Ivoire da ke zama yankinta na asali, inda ta tarbi Anastasie da wasu mata na tsohon kauyen da ta zauna.
Wata kungiya mai zaman kanta mai suna Femme de Salem ce ta yi ruwa da tsaki wajen ganin al'ummomin arewaci da kudancin Côte d' Ivoire sun yafe wa juna, tare da zama tsintsiya madaurinki daya. Ko da shi ke da farko wasu sun yi imanin cewa sulhun ba zai yiwu ba, amma Bossou Bintou Coulibaly shugabar kungiyar ta ce: "Mun san cewa a shekarun 2010 Côte d' Ivoire ta kasance cikin wadi na tsaka mai wuya, inda kasar ta rabu gida biyu bayan zabe. Mun yi tunani kan yadda za a hada kan jama'ar da suke yi wa junansu kallon banza. Sabili da haka, dole ne muka yi ta kai kawo tsakanin matan Arewa da na Kudu. Domin ta hanyar mata ne a ganinmu, za a iya yin wani yunkuri na hada kan al'umma.''
Karin Bayani: Laurent Gbagbo na gurfana gaban kotun ICC
Bayan shekaru 10 na wahala, 'yan Côte d' Ivoire baki daya na da fatan Alassane Ouattara da wanda ya gabace shi Laurent Gbagbo su magance bambance-bambancen da ke tsakaninsu. Dama kotun Côte d' Ivoire ta yankewa Gbagbo hukuncin zaman gidan yari na shekaru 20 a bayan idonsa, dangane da rawar da ta ce ya taka wajen karkata kudin babban bankin kasar BCEAO. Tuni ma Shugaba Ouattara ya nuna alamun cewa, zai yi wa Gabgbo afuwa a kan wannan batu. Geoffroy Kouao da ke sharhi kan siyasar Côte d' Ivoire ya ce wannan na nufin Gbagbo ya amince da Ouattara a matsayin shugaban kasa. Ana daukar musayar yawu tsakanin shugabannin biyu a matsayin wani muhimmin mataki na sasanta 'yan kasa, bayan rikicin zabe da ya faru shekaru 10 da suka gabata wanda ya haddasa mutuwar mutane sama da 3,000 a cewar Majalisar Dinkin Duniya.