1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun ICC ta soma zaman shari'ar Gbagbo

Abduraheem Hassan/GATJanuary 28, 2016

Kotun Hukunta Manyan Laifukan Yaki ta Duniya ta ICC ta fara zaman shari'ar tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo wanda kotun ke zargi da hannu a rikicin da kasar ta fuskanta bayan zaben shekara ta 2010.

https://p.dw.com/p/1HlSU
Fatou Bensouda babbar mai shigar da kara ta kotun ICC
Hoto: picture-alliance/dpa

A wannan Alhamis din ce Kotun ICC ta fara zaman shari'ar Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo dama na hannun damarsa Charles Ble Goude wadanda kotun ke zargi da hannun a rikicin da kasar ta fuskanta bayan zaben shekara ta 2010 da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu uku.

Sai dai Laurent Gbagbo da ke zama tsohon shugaban kasar Cote d'Ivoire, tare da tsohon ministan matasa Charles Ble Goude, sun musanta zargin da kotun ke yi masu.

Gbagbo da Ble Goude sun yi watsi da zargin da kotun ICC ke yi masa

Shi dai tsohon shugaban kasar ta Cote d'IvoireLauren Gbagbo ya furta rashin gamsuwarsa a lokacin da babban alkali Cuno Tarfusser ke masa tambayoyi a lokacin bude shari'ar. Mr. Gbagbo na cewa "ina mai amsa wannan tambaya da cewa, ban yadda ba kuma ban amince da irin wadannan tuhume-tuhume da ake a kaina na hannu a kitsa wutar rikicin da ta yi sanadiyar rayukan al'ummar Cote d'Ivoire da ma laifukan take hakkin bil'adama"

Laurent Gbagbo a gaban kotun ICC
Hoto: REUTERS/Peter Dejong

Shi ma dai dai tsohon ministan matasa Charles Ble Goude ya nuna rashin amincewarsa ne a kan laifukan da kotun ta ICC ke tuhumarsa da aikatawa inda ya ce "sam ban yi na'am da wadannan zarge-zarge da ake a kaina ba, kuma dan haka ina shaidawa duniya cewa ba na amsa laifin da ban aikata ba kuma ba ni da masaniya a kai"

Kotun ICC ta jaddada zarginta kan Gbagbo da Ble Goude

To sai dai ko kamin wannan rana, babbar mai shigar da kara a kotun ta ICC Fatou Bensouda, ta jaddada irin bincike da suka gudanar kan wadannan laifuka da suka shafi yaki da cin zarafin al'umma da ake wa tsohon shugaban na Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo.

Ble Goude a gaban kotun ICC
Hoto: Reuters/Peter Dejong

Ms. Bensouda ta ce "binciken da muke gudanarwa a kasar Cote d'Ivoire ya shafi dukkanin bangaren da suka hada da na yaki da ma take hakkin bil'adama, kuma binciken na da matukar tsaurin gaske ganin irin matakan da muke bi "

Dama dai wannan kotu na dora alhakin salwantar rayuwar mutane sama da 3,000 a kan Gbagbo a wata tarzoma da ke da alaka da zabe a shekara ta 2010. A yayin zaman kotun na yau dai, an samu halartar dimbin magoya bayan Mr. Laurent Gbagbo wanda su ka yi dafifi a harabar kotun.